Najeriya ta gargadi kamfanin Facebook game da barin kungiyar IPOB su yi amfani da dandalinsu wajen tayar da rikici da haifar da kiyayyar kabilanci a Najeriya

0 79

Ministan labarai da al’adu, Lai Mohammed, ya gargadi kamfanin Facebook da sauran kafafen sada zumunta game da barin haramtacciyar kungiyar ‘yan Biafra (IPOB) su yi amfani da dandalinsu wajen tayar da rikici da haifar da kiyayyar kabilanci a Najeriya.

Ministan ya yi wannan bukata ne jiya a Abuja a wani taro da wata tawaga ta Facebook.

Ya ce tun da aka haramta kungiyar IPOB tare da bayyana kungiyar a matsayin ‘yan ta’adda, Facebook ba shi da hujjar barin kungiyar ta ci gaba da yada farfaganda na nuna kiyayya da tada zaune tsaye a kasarnan.

Ministan ya ce duk da yawan korafe-korafen da ake yi a Facebook kan ayyukan kungiyar IPOB, babu wani abu da kamfanin ya yi na dakile wuce gona da iri da kungiyar ke yi a dandalin sada zumunta.

Lai Mohammed ya ce gwamnati za ta sanya ido sosai a kan Facebook da sauran kafafen sadarwa a cikin kwanaki masu zuwa don tabbatar da an bi wannan bukata, yayin da ta kara kaimi wajen gudanar da yakin neman zabe na amfani da kafafen sada zumunta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: