An sallami tsohon shugaban Najeriya Abdussalami Abubakar daga asibiti a birinin Landan baya wata ƴar gajeriyar jinya
An sallami tsohon shugaban Najeriya Abdussalami Abubakar daga asibiti a birinin Landan na Birtraniya, bayan da ya yi wata ƴar gajeriyar jinya.
Mai taimaka wa Shugaba Buhari kan harkokin yaɗa labarai Malam Garba Shehu ne ya faɗi hakan a shafinsa na Tuwita.
Malam Shehu ya ce shugaban ya ji sauƙi kuma jinyar da ya yi ɗin ba mai tsanani ba ce.