An Samu Rahoton Mummunan Fada A Fadin Kasar Sudan A Yayin Rikici Tsakanin Bangarorin Sojoji 2 Na Kasar

0 156

An samu rahoton mummunan fada a fadin kasar Sudan daidai lokacin da rikici tsakanin bangarorin sojoji 2 ke cigaba da yaduwa.

Fada tsakanin sojoji da ‘yan kungiyar RSF na cigaba da wakana a rana ta uku da farawa.

Wata kungiyar likitoci tace kimanin mutane 100 aka kashe yayin da aka kiyasta wadanda suka jikkata da dubu 1 da 100.

Dukkan bangarorin sun yi ikirarin iko da muhimman gurare a Khartoum, babban birnin kasar, inda mazauna birnin ke neman mafaka daga abubuwan fashewa.

Tunda farko a jiya, bangarorin sun amince da kwarya-kwaryar yarjejeniyar tsagaita wuta domin bayar da dama a kwashe wadanda aka raunata, sai dai babu tabbacin sun aiwatar da yarjejeniyar.

Likitoci sun yi gargadin cewa halin da ake ciki a asibitoci a Khartoum abin damuwa ne matuka kuma fada na hana ma’aikatan lafiya da magunguna isa ga wadanda aka jikkata. Fadan wani bangare ne na kokarin karbe mulki tsakanin shugabannin sojojin kasar, wanda ya rikide zuwa rikici tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: