An sanya ranar Talata ta zama hutun a wannan shekarar saboda shagalin murnar maulidi

0 47

Gwamnatin tarayya ta sanar da ranar Talata, 19 ga watan Oktoba ta zama hutun a wannan shekarar saboda shagalin murnar haihuwar Annabi Muhammadu SAW.

Kamar yadda ma’aikatar harkokin cikin gida ta fitar a shafinta na Facebook, sakataren ma’aikatar cikin gida, Shuaib Belgore ne a yau Juma’a

Inda ya rawaito Ministan harkokin cikin gida, Rauf Aregbesola ya na taya daukacin al’ummar musulmai murnar ganin wannan babbar rana ta wannan shekarar.

Aregbesola ya shawarci ‘yan Najeriya da su kasance masu hakuri, juriya da kaunar juna wadanda duk dabi’un annabi Muhammadu SAW ne, inda ya kara da cewa su kasance ma su yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Ya kuma yi kira akan dakatar da duk wasu abubuwan da za su janyo rabuwar kawuna a fadin kasa, inda ministan ya bukaci ‘yan Najeriya, musamman matasa su rungumi yin aiki tukuru, jajircewa akan gaskiya da zaman lafiya duk da bambance-bambancen addinai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: