An Shirya Tsaf Domin Gurfanar Da Direbobi Masu Karancin Shekaru Ko Ganganci A Lokacin Bukukuwan Sallah

0 94

Hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta ce za ta hada kai da sauran jami’an tsaro da na shari’a domin gurfanar da direbobi masu karancin shekaru da masu tukin ganganci a lokacin bukukuwan Sallah.

Kakakin hukumar na jihar Jigawa, Ibrahim Gambo ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai jiya a Dutse.

Ya ce wannan wani bangare ne na kokarin hukumar na tabbatar da zirga-zirgar ababen hawa a dukkan titunan jihar da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a yayin bikin Sallah Karama.

Ibrahim Gambo ya ce hukumar za ta fara aikin sintiri na musamman na Sallah Karamar daga yau, 20 zuwa 25 ga watan Afrilun da muke ciki. Ya bayyana cewa, kwamandan hukumar a jihar Jigawa, Ahmed TM ya bada umarnin tura dukkan ma’aikatan hukumar da kayan aiki na sintiri, domin sa ido da kuma kula da ababen hawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: