Mutane 2 Sun Mutu An Kuma Ceto Wasu Hutu A Wuse II, Abuja

0 81

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta birnin tarayya ta tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da ceto wasu mutane hudu a wata katanga da ta fadi a Ademola Adetokunbo Crescent, Wuse II, Abuja.

Babban daraktan hukumar Dr Abbas Idriss ne ya tabbatar da hakan a wata hira da kamfanin dillancin labarai na kasa jiya a Abuja.

Babban daraktan ya ce hukumar ta dade tana wayar da kan al’ummar babban birnin tarayya Abuja kan bukatar kiyayewa da dokokin gine-gine da kuma babban tsarin birnin Abuja. Ya yi kira ga masu ruwa da tsakin da ke da alhakin bayar da amincewar gine-gine a babban birnin tarayya, kamar ma’aikatar kula da ayyukan ci gaba, da sashen ayyukan injiniya da sauran hukumomi, da su tabbatar sun ba da sahihiyar amincewa tare da sanya ido kan gine-gine a dukkan wurare.

Leave a Reply

%d bloggers like this: