Ana ci gaba da aikin ceto a al’umma a kasar Indiya bayan wata gagarumar ambaliyar ruwa

0 83

Kamar yadda gidan jaridar BBCHausa ya wallafa:

Kungiyoyi daban-daban, da sojoji da hukumar kare hauɗrra da bala’i na Indiya su na ci gaba da aikin ceton wadanda suka tsira daga mummunar ambaliyar ruwan da jihar Kerala ta fuskanta a dan tsakanin nan.

Sai dai aikin na fuskantar cikas, koguna sun tumbatsa, ya yin da nan da sa’o’I hudu masu zuwa ake sa ran za a bude madatsun ruwan jihar.

Hukumomi sun ce daruruwan iyalai daga yankunan matalauta aka kwashe zuwa tudun mun tsira.

Ruwan saman da aka kwashe kwanaki ana shekawa shi ya haddasa ambaliyar ruwan, wadda ta yi sanadin mutuwar mutuwar sama da mutum 26 ciki har da yara, ya yin da ake has ashen adadin mamatan ka iya fin haka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: