Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce ana samun karuwar wadanda ke kamuwa da cutar tarin fuka wato TB da adadi mai yawa da ba a taba ganin irinsa ba cikin fiye da shekaru 10 da suka gabata.

RFI Hausa ta rawaito cewa, hukumar WHO, a cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Alhamis ta ce, karuwar masu kamuwa da tarin fukar na da nasaba da yadda annobar Korona ta hana aikin yaki da cutar a fadin duniya.

WHO ta ce yanzu haka akwai adadin mutune miliyan 4 da dubu 1 da ke fama da tarin na fuka a fadin Duniya, wanda ya kusan ninka adadin da ake da shi a shekarar 2019 na mutum miliyan 2 da dubu 900.

Hukumar ta alakanta rashin daukar matakan da suka dace a yaki da cutar a matsayin dalilin da ya ta’azzara yawan masu fama da ita, musamman bayan bullar cutar Korona da ta tilasta dakatar da yaki da sauran cututtuka masu hadari ciki har da tarin fuka.

Shugaban Hukuma Tedros Adhanom Gebreyesus, a cikin sanarwar, ya ce, karuwar masu fama da tarin fuka a Duniya, ya nuna bukatar da ake da ita wajen zage damtse a yaki da cutar mai saurin yaduwa, ta hanyar wadata asibitoci da cibiyoyin lafiya da magungunanta baya ga rigakafin dakile yaduwarta.

Shugaban sashin yaki da tarin fuka a hukamar ta WHO Tereza Kasaeva ta ce, wannan ne karon farko da ake samun karuwar masu fama da cutar daga kusan kowanne sashe na duniya tana mai cewa yanzu haka cutar ita ke matsayin ta biyu mafi lakume rayukan mutane bayan cutar Korona.

WHO ta ce a kowacce rana tarin na TB na kashe mutane da yawansu ya kai dubu 4 da 100 inda ya kashe mutane miliyan 1 da dubu dari biyar a shekarar 2020.

Karin bayani: https://www.jakadiyapress.com/2021/10/15/tarin-fuka-ya-ninku-a-duniya-inda-yake-kashe-mutane-4100-a-kullum/

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: