Shugaban jam’iyyar APC reshen Karamar Hukumar Malam Madori ya jaddada kudirin sa na biyayya ga kundin tsarin jam’iyya

0 84

Shugaban jam’iyyar APC reshen Karamar Hukumar Malam Madori Alhaji Alin Kawu, ya jaddada kudirin sa na biyayya ga kundin tsarin jam’iyya, wajen tafikarda al’amuran jam’iyyar APC domin samun nasara a zabe mai zuwa.

Shugaban ya bayyana hakane ta hannun jami’in yada labarai na karamar hukumar Alhaji Musa Muhammad Hadejia, jim kadan da kammala rantsuwar kama aiki da aka gudanar a karamar hukumar.

Alhaji Alin Kawu ya kara da cewa da shi tare dukkan wadanda aka zaba za su kawo chanjin da zai haifar da da mai ido bisa kundin tsarin jam’iyya domin samun nasara.

A jawabinsa, mataimakin Shugaban Karamar Hukumar Malam Madori Alhaji idris Abdullahi Tasko ya bukaci wadanda aka rantsar da su zamo masu gaskiya tare da biyayya ga dokokin jam’iyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: