Ana Ci Gaba Da Gwabza Fada A Sudan Duk Da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Sa’o’i 72 Da Aka Cimma

0 137

Ana ci gaba da gwabza fada a wasu sassan kasar Sudan duk da yarjejeniyar tsagaita wuta na sa’o’i 72 da aka cimma.

Da yake magana ta wayar tarho daga Omdurman, birnin da ke daura da babban birnin kasar Khartoum, wani dan jarida ya ce an gwabza fada a kusa da gine-ginen gidajen Talabijin da Rediyo.

Dan jaridar ya kara da cewa, babu mai ga karancin likitoci, kuma mutane na kokawa wajen samun abinci da takardun kudi.

Rahotanni sun ce babban hafsan sojin Sudan, Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya amince da tsawaita wa’adin tsagaita wutar da zai kare a gobe.

Abdel Fattah al-Burhan ya ba da amincewar farko ga shawarwarin da hukumar shiga tsakanin gwamnatocin Afrika ta kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta yanke. Shawarar ta nuna cewa aikewa da wakilai daga sojojin Sudan da kuma kungiyar RSF masu gaba da juna zuwa birnin Juba da ke Sudan ta Kudu domin tattauna cikakkun bayanai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: