Buhari Bai San Dimbin Alkawuran Da Kungiyoyin Goyon Baya Na Jam’iyyar APC Suka Daukarwa ‘Yan Najeriya Ba

0 53

Femi Adesina, mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, ya ce shugaban kasar bai san dimbin alkawuran da kungiyoyin goyon baya na jam’iyyar APC suka daukarwa ‘yan Najeriya ba kafin zaben shugaban kasa na 2015.

Femi Adesina ya bayyana haka ne a jiya a lokacin da ake zantawa da shi a shirin gidan talabijin na Channels.

A cewarsa, shugaban kasar bashi da hannu a mafi yawan takardun da kungiyoyin da ke goyon bayan jam’iyyar suka bayar a matsayin manufofin jam’iyyar.

Mai taimaka wa shugaban kasar, wanda kuma ya yi magana game da sace ‘yan matan Chibok, ya wanke shugaban kasar daga duk wani zargi na rashin ceto daliban gabadaya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: