Ana zargin kwamdan hisbah na Jahar Sheikh Haruna Ibn Sina da karkatar da kujerun hajjin bana ga yan uwan da makusantan sa, da kuma karbar na goro daga wasu jami’an gwamnati domin zuwa kasa mai tsarki.

Rabiu Baba Usman, mai taimakawa gwamna Abdullahi Ganduje kan hukumar hisbah,  yace an maye Gurbin sunan sa ba bisa ka’ida ba da sunan matar kwamandan hisba da dan uwan sa a kujerun hajjin da gwamnatin Jahar ta bada, duk da cewa shirye-shiryen tafiyar a ofishin sa yake.

Da farko dai mai taiwakawa gwamnan yace kwamandan hisban ya rubuta sunan sa a matsayin wadanda zasuyi aikin hajjin bana amma daga baya ya cire sunan sa ya maye dana matar sa da dan uwan sa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: