Shugaban kwamitin riƙo na jam’iyyar APC kuma gwamnan Yobe Mai Mala Buni, ya ce jam’iyyarsu na tsara yada za ta mulki Najeriya na tsawon shekara 32.

Mai Mala, ya shaida hakan ne a lokacin da ya ke naɗa mambobin kwamitin tuntuɓa da tsare-tsare jam’iyyar mai mutum 61, a sakataren jam’iyyar da ke Abuja domin daidaita tafiyar jam`iyyar kafin babban taron da za ta yi a wannan shekarar.

A cewarsa, akwai buƙatar jam’iyyar ta ci gaba da zama a mulki domin tabbatar da kuma ɗorewar tsarin dimokuradiya da ta ɗaura ƙasar a kai tun 2015.

Ya bayanan cewa jam’iyyar ta kafa wannan kwamitin ne domin shirye-shiryen cimma burinta.

Kwamitin mai mutum sittin da ɗaya ya kunshi gwamnoni da ministoci da senotoci da kuma manyan ƴan siyasa, kuma an danka wa gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar jagorancinsa.

Jam’iyyar dai ta yi fama da rigingimun cikin gida gabannin nada Gwamnan jihar Yobe Maimala Buni a matsayin shugaban kwamitin rikon jam’iyyar.

Sannan ya shaida cewa jam’iyyar na ƙoƙarin ganin yada za ta tafi tare da kowanne shugaba a matakai daban-daban.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: