A wani labarin makamancin wannan, daliban makarantun sakandare na gwamnati na jihohin Sokoto da Zamfara ba za su rubuta jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WAEC) ta watan Mayu da Yunin bana.

Shugaban ofishin hukumar jarabawar yammacin Afrika ta kasa (WAEC), Patrick Areghan, wanda ya bayyana hakan a jiya, bai bayyana dalilan matakin ba.

Amma an bayyana cewa hukumar jarabawar ta ki karbar dalibai daga jihar Zamfara bisa wasu basussuka da ake bin jihar tsawon shekaru.

Majiya mai tushe ta tabbatar da yadda gwamnatin tsohon gwamnan jihar, Abdulaziz Yari, ta ki biyan hukumar jarabawar kudaden daliban da suka dauki nauyin jarrabawar.

Sai dai wannan shi ne karo na biyu da daliban jihar Sokoto na makarantun gwamnati ba za su rubuta jarrabawar ba, kasancewar gwamnati ta gaza gabatar da dalibai a bara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: