Labarai

Yan bindiga sun kashe mutane 3 a garin Gurbin Magarya na karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina tare da raunata mutum 3

Yan bindiga sun kashe mutane 3 a garin Gurbin Magarya na karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina, tare da raunata mutum 3.

An bada rahotan cewa yan bindigar sun kashe dabbobi 3 a lokacin da suka kaiwa garin hari.

Manema Labarai sun rawaito cewa yan bindigar sun kaiwa garin hari ne da Misalin karfe 10 na Dare a lokacin da mutane suke Bacci.

Wani mazaunin garin Jibia mai suna Halliru Haladu, ya fadawa manema labarai cewa sun kai harin ne akan Babura.

An bada sunayen mutanen da aka kashe da Muntari Naqawuri, da Surajo Salisu da Musa Hassan.

Kawo yanzu, kakakin rundunar yan sandan Jihar Katsina SP Gambo Isah, bai amsa kiran wayar da aka masa ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: