

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Shugaban Kasar Somalia Mohammad Abdullahi Farmajo, ya sanar da kudurin sa na sake tsayawa kujerar shugaban kasar a karo na biyu a zaben da za’a gudanar ranar 15 ga watan Mayun wannan shekara.
Mista Farmajo, ya ce zai yi takarar ne biyo bayan kiraye-kirayen da al’umma suke masa na ya sake tsayawa takarar a karo na biyu domin cigaba da gudanar da ayyukan raya kasa.
Wa’adin Mista Farmajo ya kare ne a watan Fabreru na shekarar 2021, amma aka tsawaita kara masa lokaci saboda zaben majalisar kasar.
Mambobin Majalisar Somalia ne suke zabar shugaban kasa, domin ya jagoranci kasar.
Shugaba Farmajo zai fafata ne da sauran yan takarkaru domin ciki harda tsoffin shugabannin kasa.