Babban bankin kasa CBN, ya mayarwa gwamnatin jihar jigawa ginin matsugunin wucin-gadi na bankin dake Dutse.

Kwanturolan reshen bankin dake Dutse, Hajiya Sa’adatu Ibrahim wacce ta mika makulan ginin ga Sakataren Gwamnatin Jiha, Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini, ta ce bankin ya na matukar farin cikin mayarwa gwamnatin jiha ginin, bayan da bankin ya tare matsunin sa na din-din-din.

Kwanturolan wacce ta sami wakilcin daya daga cikin manyan ma’aikatan bankin, Muhammad Sani, ta bayyana farin cikin babban bankin ga gwamnatin jihar jigawa a madadin gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele.

Da yake karbar makulan ginin, sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Adamu Abdulkadir Fanini, ya yabawa babban bankin bisa mayarwa gwamnati kayanta, inda ya yaba musu dangane da gina ofishin bankin na din-din-din a Dutse.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: