Labarai

Babban bankin kasa (CBN) ya yi kira ga manoman da suka ki biyan basussukan da aka basu a karkashin shirin Anchor Borrowers da su biya

Babban bankin kasa (CBN) ya yi kira ga manoman da suka ki biyan basussukan da aka basu a karkashin shirin Anchor Borrowers da su biya.

Wani ma’aikaci a ofishin hada-hadar kudi na CBN, Sadeeq Ajayi, ya yi wannan roko a jiya a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Shirin Anchor Borrowers’ shiri ne na rancen noma da gwamnatin tarayya ta kaddamar a shekarar 2015, karkashin CBN, domin bayar da lamuni ga kananan manoma.

Sadeeq Ajayi ya ce galibin manoman jihar Oyo da suka ci gajiyar shirin ba su biya bashin da aka basu ba.

Ya ce gazawar babban bankin na karbo bashin daga hannun manoman da suka ki biya, yana barazana ga dorewar shirin, inda ya ce hakan ya hana sauran manoma samun nasu rancen.

Sadeeq Ajayi ya ce ya kamata masu ruwa da tsaki ciki har da masu rike da sarautun gargajiya su yi kira ga manoman da suka ki biya da su gaggauta biya bashin domin wasu ma su amfana.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: