Labarai

Dakarun Operation Delta Safe da sun gano tare da lalata haramtattun matatun man fetur guda 167 a yankin Neja Delta cikin makonni 3

Helkwatar tsaro tace dakarun Operation Delta Safe da na Operation Dakatar da Barawo, sun gano tare da lalata haramtattun matatun man fetur guda 167 a yankin Neja Delta cikin makonni 3.

Daraktan yada labaran tsaro, Manjo Janar Bernard Onyeuko, shine ya sanar da haka a yau yayin da yake jawabi ga manema labarai akan ayyukan dakarun sojoji tsakanin ranar 28 ga watan Afrilu zuwa 19 ga watan Mayu a Abuja.

A Operation Delta Safe, Bernard Onyeuko, yace dakarun soja sun lalata haramtattun matatun mai guda 17 tare da kwale-kwalen katako guda 5, da tankunan ajiya guda 89 da abun gashi guda 59, da ramuka 12 da injinan jawo mai guda 6 da manyan motoci 5 da injinan ruwa guda 2 da makamai 2.

Yace an kuma kwato jumillar lita dubu 778 da 500 ta danyen mai, lita dubu 840 da 300 ta man Gas da lita 625 ta kalanzir.

Ya kara da cewa an kuma kama bata gari 18 cikin makonnin, inda ya kara da cewa dukkan abubuwan da aka kwato da wadanda aka kama, an mika su ga hukumomin da suka dace domin cigaba da bincike.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: