Bakin Hali Ya Janyo An Kori Wasu Ma’aikatan Lafiya 3, Duba Laifin Da Suka Aikata

0 112

Babban asibitin koyarwa na Gwamnatin tarayya dake jihar Katsina ya salami wasu ma’aikatansa 3 bayan da aka kama su da laifin karbar kudade a wajen marasa lafiya.

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban sashin mulki na asibitin Abdurrahman Samaila ya rabawa manema labarai a jihat Katsina ta ce sallamar ma’aikatan su 3 ya biyo bayan sakamakon binciken da aka gudanar.

Samaila y ace hukumar asibitin ta gudanar da bincike mai zurfi kan dabi’un ma’aikatan Kafin yanke wannan hukunci domin kare marasa lafiyar daga bata gari.

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewa hukumar asibitin ta samar da wata sabuwar hanyar sadarwa ta latironi domin duba yadda ake biyan kudade a asibitin inda dukkanin nau’rorin ke hade da sabon tsarin fasahar. Babban daraktan asibitin Dr. Suleman Bello y ace sabuwar fasahar zata taimaka wajen rage yawan jira da kuma cinkoso biyan kudade a asibitin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: