Jinjina Ga Yan Najeriya Da Kuka Ki shiga Tafiyar Juyin Juya Hali – Garba Shehu

0 100

Fadar shugaban kasa ta yabawa ‘yan Najeriya wajen kare martabar demokradiyyar kasar nan, bayan da suka ki amincewa da kiran kungiyar Global Colaliation For Security And Democracy In Nigeria wanda ke ikirarin ayi juyin mulki a Najeriya.

Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin watsa labarai Malam Garba Shehu shi ne ya bayyana hakan inda ya ce milyoyin ‘yan Najeriya ne suka yi watsi da batun tare da maida hankali kan harkokin kasuwancinsu.

Garba Shehu ya ce kungiyar tayi yunkurin sanya yan Najeriya shiga cikin yunkurin neman ayi juyin mulki, wanda hakan wata hanya ce ta zubar da damar su ta mulkin demokradiyya.

A wani labarin kuma kungiyar matasan Arewa ta tarayyar Najeriya tayi watsi da kiran na kungiyar mai neman ayi juyin mulki, inda ta shawarci matasa da kada su yadda ayi amfani da su wajen wannan al’amari.

Shugaban kungiyar Adamu Kabir Matazu ya bayyan hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja. Kazalika Matazu ya yabawa jami’an tsaro na farin kaya wajen tarwatsa masu zanga zangar neman wannan kuduri tare da kame su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: