Bama amfani da jerin gwanon motoci domin rage kashe kudaden gudanar da gwamnati

0 88

Gwamnan Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, yace a yanzu gwamnoni basa amfani da jerin gwanon motoci da motoci 30 zuwa 40, a matsayin matakin rage kashe kudaden gudanar da gwamnati.

Da ake fira da shi a gidan talabijin na Channels, wanda aka watsa a jiya, gwamnan yace takwarorinsa na daukar manyan matakai da nufin rage kashe kudaden da ba na tilas ba a jihoshinsu.

Yayi bayanin cewa akan a dinga ciyo bashin kudade domin kashewa, gwamnonin jihoshi na mayar da hankali wajen daukar ma’aikata a bangarorin ilimi da kiwon lafiya.

A cewarsa, dayawa daga cikin gwamnoni basa daukar ma’aikatan da aikinsu baya shafar rayuwar mutane kai tsaye.

Ya kuma musanta rade-radin cewa gwamnoni suna kwashe makudan kudade domin kula da tsaro a jihoshinsu.

Gwamnan ya bayyana cewa duk da kasancewar yawan kudaden da ake warewa na kula da tsaro ya ragu sosai, wasu daga cikin gwamnonin ma basa samun kudaden kwata-kwata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: