Shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Adamu, yace jam’iyyar bata danasanin sanya naira miliyan 100 a matsayin kudin sayen Fom din, nuna sha’awar tsayawa takarar shugabanci kasa a zaben 2023.

Abdullahi Adamu, ya bayyana hakan ne a juma’a, a fadar shugaban kasa dake babban birnin tarayya Abuja, bayan ya gabatar da dan takarar gwamnan jihar Ekiti a tutar jam’iyyar APC Abiodun Oyebanji ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewarsa sun sanya kudin Fom din ne domin kashe gwaiwar wadanda bada gaske suke ba, domin kuma jam’iyyar ta samu wadataccen kudin da zata shiga babban zaben 2023.

Ya kara da cewa sanya Naira miliyan 100 a matsayin kudin Fom, zai kara kashe gwaiwar jam’iyyun adawa, domin APC ta samu nasara a zaben 2023.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: