Jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu, ya sayi Fom din nuna sha’awar tsayawa takara a jam’iyyar APC, bayan ya biya Naira miliyan 100 a yau Juma’a.

Manema labarai sun gano cewa Tunubu, wanda yanzu haka yake kasar Saudi Arabia, wasu na hannun daman sa ne suka jagoranci sayo masa Fom din.

Wadanda suka hada da dan majalissar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar Agege dake jihar Legas James Faleke, Sanata Babatunde Adejare, sai kuma tsohon sakataren gwamnatin tarayya Babachir Lawal.

Kafin hakan dai Tunubu ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar ne a watan Mayu bana, bayan ya kammala ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tunubu ya kasance mutum na uku a halin yanzu daya mallaki Fom din tsayawa takarar shugabancin kasa a jam’iyyar APC, bayan karamin ministan Ilimi Emeka Nwajiuba da kuma gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: