Gwamnatin tarayya ta ayyana ranar Litinin 2 ga watan Mayu da kuma Talata 3 ga watan Mayu a matsayin ranakun hutun Sallah ta bana da kuma ranar ma’aikata ta bana.

Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya bayyana hakan a jiya, amadadin gwamnatin tarayya.

Ya kuma taya ma’aikata dake fadin kasar nan murnar, bisa irin namijin kokarin sukeyi wajan gudanar da ayyukansu.

Ya kara da cewa kwazon aikin sune yasa kasar nan take samun nasarori a kowanne bangare, tare da daga likafar kasar nan a idon duniya.

Ministan ya kuma bukaci musulmai da suyi amfani da bikin Sallar, wajan yin adduar zaman lafiya tare da adduar Allah ya albarkaci Nijeriya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: