Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa reshen Jihar Jigawa, ta shigar da karar Manoma 300 a Kotu, saboda gaza biyan kudaden bashin da suka ara a wurin kungiyar da nufin yin Noma.

Shugaban Kungiyar na Jihar Jigawa Alhaji Adamu Haruna Maigoro Hadejia, shine ya bayyana hakan inda ya kara da cewa wasu Manoman sun fara dawowa da kudaden da suka karba na Bashin.

A cewarsa wanda sukaki su kawo kudaden da suka karba bashi a hannun Kungiyar yanzu haka suna dawowa dashi, saboda kotu da umarcesu.

Haka kuma ya ce kungiyar tana sane da sunayen mutane 500 da sukaki su dawowa da kudaden da suka karba.

Kazalika ya ce kimanin manoma dubu 1,887 ne suka karbi kayan Noma wanda suka hada da Takin Zamani da Magani da kuma kuma Injin feshi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: