Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta amince da kafa wata sabuwar hukuma da zata yaki cin hanci da rashawa.
Sabuwar hukumar wacce majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da ita, za a dora mata nauyin kula da dukkan kadarorin satar da aka kwato.
Ministan shari’ah kuma babban lauyan tarayya, Abubakar Malami, ya sanar da haka ga manema labaran fadar shugaban kasa, bayan zaman ganawar majalisar zartarwa ta tarayya wanda aka gudanar a jiya laraba.
- Tinubu ya ziyarci jihar Kaduna domin ƙaddamar da wasu ayyuka a jihar
- NEMA ta tarbi ƴan Najeriya 147 da aka dawo da su daga Nijar
- Najeriya za ta kwashe mutanenta daga Isra’ila da Iran
- INEC ta yi watsi da sanarwar taron NEC na Jam’iyyar PDP
- Gwamnatin Jigawa ta ware naira biliyan 2 domin gina magudanan Ruwa da Gadaje
Yace sabuwar hukumar za ta sake bibiyar yadda ake kula da kadarori da dukiyoyin da aka kwato daga hannun marasa gaskiya.
Ministan yace majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da aikawa da kudirin neman kafa hukumar zuwa ga majalisar kasa.