Buba Marwa yace matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar mutane a Najeriya na kan hanyar zuwa karshe

0 104

Shugaban hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) Buba Marwa, yace matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da safarar mutane a Najeriya na kan hanyar zuwa karshe.

Bubar Marwa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na kasa a Birnin New York na Amurka cewe da tallafin gwamnatin tarayya da abokan huldar kasashen waje, da masu ruwa da tsaki, Najeriya za ta iya samun nasara a yaki da shan miyagun kwayoyi da safarar mutane.

Bubar Marwa yace ofishin majalisar dinkin duniya mai kula da kwayoyi da aikata laifuka yana tallafawa Najeriya a yakin da take yi da shaye-shaye, musamman ta hanyar horas da ma’aikatan hukumar da bayar da bayanai.

Yace gwamnatin tarayya ta samar da jadawalin magance shaye-shaye na kasa na shekarar 2021 zuwa 2025 wanda aka gyara, tare da tallafin majalisar dinkin duniya mai kula da kwayoyi da aikata laifuka da tarayyar Turai.

Da yake magana dangane da yiwuwar noman tabar wiwi da nufin habaka tattalin arzikin kasarnan, shugaban na NDLEA yace hukumar bata goyon bayan halasta noman tabar wiwi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: