Manoman shinkafa a nan jihar Jigawa sun ce tsuntsayen da suka mamaye gonakinsu sun zama babbar barazana ga noman shinkafa a jiharnan.

Wasu manoman shinkafa ne suka sanar da haka a kauyen Gatafa dake Karamar hukumar Auyo a lokacin da ake aikin feshin maganin tsuntsayen.

Manoman sun ce harin da tsuntsayen ke kaiwa gonakinsu na shinkafa wani bangare ne na babbar barazanar da manoma ke fuskanta a kowace shekara.

Sai dai, sun yabawa gwamnatin tarayya da ta jiha bisa aikin feshin maganin tsuntsayen.

Babban Mai Taimakawa Gwamna Muhammadu Badaru Abubakar akan shigo da al’umma cikin gwamnatin, Hamza Muhammad Hadejia, yace aikin feshin maganin tsuntsayen ya biyo bayan korafin da manoma ke yi dangane da mamayar da tsuntsayen suka yiwa gonakinsu.

Yayi bayanin cewa anyi feshin maganin tsuntsayen a kananan hukumomin 11 na jiharnan, tare da hadin gwiwar gwamnatin jiha da ta tarayya.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: