Buhari Yayi Alhinin Mutuwar Tsohon Atoni-Janar Bola Ajibola

0 108

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan tsohon Atoni Janar kuma ministan shari’a, Prince Bola Ajibola, SAN, wanda ya rasu yana da shekaru 89 a duniya.
A lokacin da yake jajanta wa kungiyoyin lauyoyi ta Najeriya da ma duniya baki daya, shugaba Buhari ya bayyana cewa fitaccen lauyan ya yi amfani da ilimi da basirar da Allah ya ba shi wajen tabbatar da adalci da gaskiya da daidaito a dukkan ayyukansa a ciki da wajen Najeriya.
Shahararren alkalin ya kasance a lokuta daban-daban, Shugaban Kungiyar Lauyoyin Najeriya (1984-1985), ya taba zama Shugaban Kungiyar Alkalai ta Duniya, sannan Shugaban Kungiyar Manyan Lauyoyin Najeriya da kuma Shugaban Kotun Gudanarwa na Bankin Duniya da sauran manyan nasarori.
Shugaba Buhari ya ce, Marigayi Ajibola, bayan ya kai ga kololuwar sana’arsa, ya kai hazakarsa ta fuskar shari’a zuwa kotun kasa da kasa da ke Hague, inda ya yi aiki tukuru a tsakanin 1991 zuwa 1994. Ya kuma kasance babban kwamishinan Najeriya a fannin shari’a a Ingila, 1999 zuwa 2002.
Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai Femi Adesina ya fitar, ta ruwaito Buhari na cewa ba za a iya wuce gona da iri irin gudunmawar da ya bayar wajen bunkasa harkokin shari’a ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: