Jiragen Yakin Isra’ila Sun Kai Hari Kan Makaman Sojin Syria

0 93

Isra’ila ta ce jiragen yaƙinta sun kai hari kan makaman atilari da makamai masu linzamin da sojin Syria suka harbo.
Tun da fari, kafar yaɗa labaran Syria ta ce an ji ƙarar fashewar wani abu a kusa da birnin Damascus, ya yin da rahotanni ke cewa Isra’ila na kai hare-hare ta sama babu ƙaƙƙautawa a birnin.
Sojojin Isra’ila sun ce sun harbo makaman roka shida kusa da Isra’ila, ya yin da wasu suka faɗa tuddan Golan, kuma alhakin duk abin da ya faru a iyakarta ya rataya ga gwamnatin Syria.
A kwanakin nan, mayakan ƙungiyar Hamas sun yi ta harba makaman roka zuwa Isra’ila daga Falasɗinu da Lebanon, ya yin da ita kuma ke maida martani da lugude ta sama.
Ministan tsaron Israel ya tabbatar da harin a shafin sa na Facebook.
Sai dai yace ba’a samu wanda ya jikkata ba yayin harin, in banda gine-gine da dukiyoyin al’uma da suka lalace.
A wani wajen daban kuwa, daruruwan Falasdinawa sun tare a masallacin Al-Aqsa dake gabashin Jerusalem yayin da yan sandan isarl’ila ke kai farmaki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: