Datti Na Labour Party Yaki Amincewa Da Kiran Da Akayi Na Muhawara Da Wole Soyinka

0 51

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour, Yusuf Datti Baba-Ahmed a zaben fabarerun 2023, ya ki amincewa da kiran da aka yi na muhawarar da fitaccen dan Najeriya, Farfesa Wole Soyinka.
Baba-Ahmed ya sha suka a kan kalaman da ya yi a gidan Talabijin na Channels a watan da ya gabata, cewa ba dace a rantsar da Ahmed Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya ba a ranar 29 ga Mayu.
Da yake mayar da martani ga kalaman Baba-Ahmed, Soyinka ya bayyana shi a matsayin farkisanci.
A ranar Juma’a, Soyinka, ya kalubalanci dan takarar mataimakin shugaban kasar na jam’iyyar labour zuwa teburin muhawara.
Sai dai, Baba-Ahmed, a wata sanarwa da ofishin yada labarai na Obi-Datti ya fitar ranar Asabar, ya ce ba zai iya karbar tayin Soyinka na muhawara ba saboda dalilai na siyasa da kuma zamantakewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: