Yan Fashin Dajin Da Suka Sace Mata A Zamfara Sun Nemi Kudin Fansa N30M

0 106

‘Yan fashin dajin da suka sace gomman yara da mata a ƙauyen Wanzamai na jihar Zamfara sun nemi a biya kuɗin fansa, kamar yadda wasu daga cikin wadanda lamarin ya shafa suka sanar da jaridar daily trust.
Yan bindigar a ranar alhamis sun sace akalla mutane 100 a gonaki a jihohin Zamfara da Katsina.
Wani dan garin Wanzamai dake karamar hakumar Tsafe a JIHAR Zamfara yace yaran da akayi garkuwa dasu a garinsu sun kai 80 yayin da aka sace wasu sama 20 a makobtan garuruwa.
Wata majiya tace yan bindugar sun fara tuntubar iyalan wasu daga cikin wadanda akayi garku da su suna neman kudin fansa naira miliyan 60 kafin a saki yaran, sai an karkare a naira miliyan 30.
Haka kuma kakakin rundunar yansandan jihar SP Muhammad Shehu yace kwamashinan yan sandan jihar ya tabbatarwa iyalan wadanda lamarin ya shafa yunkurin da hakumar yan sanda ke yi domin kubutar da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: