Yan Sanda Sun Kama Mutum 7 Da Ake Zargin Yan Fashi Ne A Bauchi

0 92

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta kama wasu mutane 7 da ake zargin yan fashi ne a maboyar su dake unguwar Magaji.
Rundunar yan sandan tace wadanda ake zargin basu wuce tsakanin shekaru 17 zuwa 25, an same su da makamai masu hatsari da kuma Barasa.
A wata sanarwa da kakakin rundunar yan sandan jihar Ahmed Mohammed Wakil ya fitar, tace wadanda ake zargin sun hada Rayyanu Mohammed, Mustapha Harisu, Yusuf Ibrahim, Mubarak Lawal, Abubakar Musa, Al-Amin Hussaini da kuma Hamza Umar.
Kamen ya biyo bayan bayanan sirri da hakumar yan sanda tace ta samu tare da hadin guiwa da jami’an sa kai.
A cewar kakakin yan sandan, binciken farko ya nuna wanda ake zargin yan wata kungiya ne mai suna Sara Suka dake gudanar da ayyukan su a cikin kwaryar birnin Bauchi.
Da yake magana dangane da kamen kwamashinan yan sandan jihar Aminu Alhassan, ya roki iyaye da dukkan masu ruwa da tsaki da suke sanya idanu akan yaransu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: