Covid-19 Yadda titunan Abuja suka zama wayam tamkar kufai.

0 65

A yayinda aka sanya dokar hana fita a wasu yankunan kasar a kokarin da ake na hana yaduwar cutar coronavirus, an gano titunan Abuja, Babban Birnin Tarayyar Najeriya sun zama tamkar kufai, inda ko ina ya zama wayam babu mutane.

Hakan ta kasance ne a ranar Talata,31 ga watan Maris, bayan dokar da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya ta hana fita ta soma aiki.

A jawabin da shugaba Buhari ya yi a karshen makon da ya gabata, ya umarci a rufe biranen Abuja, Lagos da kuma Ogun na tsawon mako biyu a wani matakin hana yaduwar coronavirus.

Ya zuwa yanzu dai mutum 139 ne suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 82 a jihar Legas yayin da mutanen da suka kamu da cutar a Abuja ya kai kimanin mutum 28.


Abdullahi Yawale

Leave a Reply

%d bloggers like this: