Kasar Indiya tana ci gaba da kasancewa inda ake samu yaduwar cutar coronavirus tsakanin kasashen duniya tun daga makon da ya shude inda ake da rabin sabbin kamuwa aka samu a kasar, inda kimanin mutane 3,780 cutar ta halaka a kwana guda a kasar da ke yankin kudancin Asiya.

Hukumar kula da lafiya ta duniya ta ce kashi 46 cikin 100 na sabbin kamuwa da coronavbirus tun daga makon jiya a Indiya aka samu kowace rana sama da mutane 300,000 ke kamuwa da cutar. Tuni asibitoci suka shake da marasa lafiya kuma babu gadajen da za a saka sabbin marasa lafiya.

Gwamnatin Firaminista Narendra Modi tana shan suka kan hanyoyin da ta tunkari wannan annoba, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da taimakon kasar kan magance matsalar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: