Najeriya tana fuskantar sake bullar COVID-19 saboda raguwar masu karbar rigakafi

0 88

Rahotanni daga Najeriya, kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka na cewa, kasar na fuskantar barazanar sake bullar annobar COVID-19, a gabar da adadin wadanda ake fatan yiwa rigakafin a shekara ya ragu.

Kwamishinan lafiya na jihar Lagos Akin Abayomi, ya bayyana cewa, a Lagos, cibiyar kasuwancin kasar, kana inda cutar ta fi kamari, kimanin mutane 260,000 ne suka karbi rigakafin, kaso 1 kacal cikin 100 na yawan al’ummar jihar.

Hukumar lafiya a matakin farko ta kasar, ta ce ya zuwa ranar Talata, mutane miliyan 1.2 ne kawai aka yiwa rigakafin.

A ranar 5 ga watan Maris din da ya gabata ne dai, aka fara yiwa ‘yan kasar rigakafin annobar, da kason farko na allurai miliyan 3.94 na kamfanin AstraZeneca da kasar ta samu karkashin shirin nan na COVAX.

Leave a Reply

%d bloggers like this: