Dakarun Hadin Gwiwa sun kashe kimanin mayakan kungiyar Boko Haram 100 tare da manyan kwamandojin su 10 a yankin Tafkin Chadi

0 44

Dakarun Hadin Gwiwa sun kashe kimanin Mayakan Kungiyar Boko Haram 100 tare da Manyan Kwamandojin su 10 a yankin Tafkin Chadi.

Shugaban Sashen Yada Labarai na Rundunar Kanal Muhammad Dole, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, inda ya ce Sojojin sun samu nasarar hakan ne bayan hadin gwiwa tsakanin Sojojin Sama dana Kasa.

Kanal Dole, ya ce Dakarun kawancen Najeriya, Nijar da kuma Kamaru ne suka samu nasarar aiwatar da aikin.

Haka kuma ya ce Dakarun Sojan Saman Najeriya da na Kasa da kuma sauran hukumomin tsaro ne suka tallafa wajen dakile maharan.

Sanarwar ta ce Dakarun sun samu nasarar ne biyo bayan bayanan sirri da suka samu kan ayyukan yan ta’addar.

Kakakin Rundunar ya ce sun yi nasarar kwato kayayyakin Abinci, wanda suka hada da Masara, Wake, Shinkafa da kuma Babura a yankin na Fedondiya da ke Jihar Borno.

Leave a Reply

%d bloggers like this: