Labarai

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sanar da amincewa da karin kashi 30% na albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai da ke jihar

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya sanar da amincewa da karin kashi 30% na albashin likitoci a kananan hukumomi bakwai da ke jihar.

Zulum Ya bayyana hakan ne a wata ziyarar da ya kai da daddare a babban asibitin Monguno a ranar Asabar.

Baya ga likitoci, ma’aikatan jinya, ungozoma, kwararrun dakin gwaje-gwaje, likitoci da sauran ma’aikatan lafiya na kananan hukumomin bakwai za su ci gajiyar karin kashi 20% na albashi da nufin zaburar da su wajen gudanar da ayyukan kiwon lafiya masu inganci da araha.

Kananan hukumomi bakwai sun hada da, Monguno, Ngala, Dikwa, Kukawa, Kala-Balge Abadam da kuma Banki.

Gwamnan ya kuma ba da umarnin gina karin rukunin ma’aikata da samar da rijiyoyin burtsatse masu zurfi da kuma hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana don inganta ayyuka a wurin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: