Karamar Hukumar Kirikasamma ta kashe kudi fiye da naira 1,850,000 wajen tallafawa shugabannin jam’iyyar APC a matsayin tallafin azumi

0 20

Karamar Hukumar Kirikasamma, ta kashe kudi fiye da naira miliyan daya da dubu dari takwas da hamsin wajen tallafawa shugabannin jamiyyar APC da kuma sauran masu ruwa da tsaki a matsayin tallafin azumi.

Shugaban Karamar Hukumar, Alhaji Isa Adamu Matara ne ya sanar da hakan ga jamiin yada labarai na yankin, inda yace an raba tallafin azumin ne ga shugabannin jamiyyar na mazabu da dattawan jamiyya domin sayen Sukarin azumi.

Ya gargadi shugabannin jamiyyar dasu sanya tsotan Allah wajen rabon kudaden ga yan jamiyya.

Alhaji Isa Adamu Matara, ya kara da cewar, kowacce mazaba ta samu tallafin naira dubu dari da 85 domin rabawa shugabanni da dattawan jamiyya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: