Labarai

Gwamnatin jihar Jigawa tana gudanar da aiyukan mazabu na kimanin naira miliyan dari a sassa daban-daban na karamar hukumar Gumel

Gwamnatin jihar Jigawa tana gudanar da aiyukan mazabu na kimanin naira miliyan dari a sassa daban daban na karamar hukumar Gumel.

Wakilin mazabar Gumel, a majalissar dokokin jiha, Alhaji Sani Isyaku Abubakar, ya sanar da hakan a lokacin dayake zantawa da kamfanin dillacin labarai na kasa NAN a birnin Dutse.

Yace, aiyukan mazabun na 2021, da aka gudanar a mazabarsa, sun hadar da gina masalatan juma-a na Kokinami da Danfarantama yayinda ake gudanar da aikin gina masalacin juma-a na unguwar Dantanoma.

Alhaji Sani Isyaku, ya kara da cewar sauran aiyukan mazabun sun hadar da aikin gina makarantun Islamiyya a Ubandawaki da kuma unguwar Abuja Gumel da aikin gyaran masalatan kamsisalawati na tsohan asibiti dake garin Gumel da garin Gangara.

Ya kara da cewar aiyukan mazabun suna da muhimmanci wajen cigaban rayuwar alumma musamman mazauna yankunan karkara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: