Labarai

Yadda wasu yan ta’adda suka kai hari kauyukan Gwada da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja a lokacin da musulmi suke shirin buda baki

Yan ta’adda sun kai hari a kauyukan Gwada da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Neja a lokacin da musulmi suke shirin buda baki, na azumin watan Ramadana a ranar Asabar.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya tattaro cewa maharan sun kashe mutane hudu tare da yin awon gaba da mutanen da ba a tantance adadinsu ba.

Kakakin Gamayyar Kungiyoyin Shiroro, Salisu Sabo, wanda ya tabbatar wa da wakilinmu harin ta wayar tarho, ya ce ‘yan ta’addan sun shafe sa’o’i da yawa suna ta’addanci a cikin al’umma.

Ya ce ‘yan ta’addan sun fatattaki al’ummomin da ke kan hanyar Gwada zuwa Shiroro.

Al’ummomin sun hada da Tapila, Kwakwa, Kadna da kuma garin Gwada, wanda yana daga cikin wuraren da babu tsaro a karamar hukumar Shiroro.

Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kawo musu dauki ta hanyar tura karin jami’an tsaro a yankin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: