Ministan Sadarwa Isah Pantami ya ce akwai buƙatar al’ummar Musulmi su ƙara gina masallatai da cibiyoyin Musulunci don bunƙasa addinin

0 131

Ministan Sadarwa da Bunkasar Tattalin Arzikin na Fasahar Sadarwa Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, ya ce akwai buƙatar al’ummar Musulmi su ƙara gina masallatai da cibiyoyin Musulunci don bunƙasa addinin.

Farfesa Pantami ya bayyana haka ne a yayin wani taro na gabatar da rahoton aikin faɗaɗa Masallacin An-Noor da aka yi a Cibiyar Musulunci da Ilimi ta Ƙasa da Ƙasa, ICICE, Abuja, ranar Asabar.

Ya ce a tarihi masallatai ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ilimin addinin Muslunci, yana mai cewa, jami’ar farko da aka kafa a duniya ta samo asali ne daga masallaci.

A cewarsa Jami’a ta biyu da aka kafa a duniya gaba ɗaya ta samo asali ne daga masallaci. Haka kuma, jami’ar farko mai bada digiri a duniya ita ce Jami’ar al-Qarawiyyin, Moroko.

Haka kuma ya ce bayan ita kuma sai Jami’ar Azhar dake Alƙahira, Masar, duk sun samo asali daga masallaci.

Kazalika, ya ce wannan yana nuna mana masallaci ba kawai wajen da ake haɗuwa a yi salloli biyar ba ne, ya kamata masallaci ya zama wajen koyon ilimi, wajen tarbiyyantar da yara, wajen haɗa kan Musulmi, kuma cibiyar bada jagoranci da shawarwari.

Leave a Reply

%d bloggers like this: