Daliban firamare 490,874 ne na fadin jihar Jigawa suke cin gajiyar shirin Gwamnatin tarayya na ciyarwa

0 119

Kimanin Daliban Makarantun Firamare dubu 490,874 ne na kananan hukumomin 27 na Jihar Jigawa suke cin gajiyar shirin Gwamnatin tarayya na ciyarwa.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Jinkai, Iftila’i da Cigaban Al’umma Misis Rhoda Iliya Ishiku ta rabawa manema labarai a Abuja.

A cewarta, Babban Sakatare a Ma’aikatar Alhaji Nura Alkali, shine ya bayyana hakan, inda ya ce a jihar Jigawa kadai gwamnatin tarayya tana aiwatar da shirin a Makarantun Firamare dubu 2,180 ta kuma dauki Masu girki dubu 5,267 a kananan hukumomi 27 na jihar nan.

Alhaji Nura Alkali, ya ce hakan kari ne akan Kwanika dubu 500,000 wanda gwamnatin tarayya ta samar a shekarar 2018 a Jihar Jigawa domin a rika zubawa Daliban Abinci a ciki.

Haka kuma ya ce an kirkiri shirin ne domin a magance matsalar talauci, shirin kuma hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin tarayya da sauran Jihohi.

A jawabinsa, Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya godewa gwamnatin tarayya bisa kirkirar shirin, inda ya bukaci a kara tallafawa masu karamin karfi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: