Dalilan da yasa Buhari ya miƙa wa majalisun dokokin Najeriya buƙatar gyaran dokar kasafin kuɗi na 2022

0 164

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya miƙa wa majalisun dokokin ƙasar buƙatar gyaran dokar kasafin kuɗi ta 2022 a yau Talata.

Buƙatar neman gyaran ta biyo bayan dakatar da Dokar Man Fetur ce, wadda ta tanadi a soke biyan tallafin man fetur ɗin da kuma mayar da harkar mai ta ‘yan kasuwa zalla.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da shugaban ya rubuta wa ‘yan majalisar wadda kuma Shugaban Majalisa Sanata Ahmad Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila suka karanta a zaurukan majalisunsu.

Gwamnati na neman majalisar ta amince da ƙarin fiye da naira tiriliyan biyu da Biliyan 557 don biyan kuɗin tallafin mai daga Yuli zuwa Disamban 2022 da kuma sake duba Dokar Kuɗi ta Finance Act 2021.

A cikin wasiƙar, Buhari ya ce gyaran ya zama dole don ƙara wasu ayyuka a ciki da suka haɗa da tallafin man fetur, wanda tun farko gwamnatinsa ta yi niyyar daina biya kafin daga baya ta sauya shawara. Tun da farko gwamnatin tarayya ta tanadi kuɗin tallafin na wata shidan farko na shekarar 2022 a kasafin kuɗin, inda aka ware biliyan Naira 443 daga Janairu zuwa Yunin 2022.

Leave a Reply

%d bloggers like this: