Dalilan da yasa EFFC ta garkame gidan tsohon gwamnan Kano, Rabiu Kwankwaso

0 45

Hukumar Yaki da Cin Hanci Da Rashawa (EFCC) ta kulle wani gini mallakin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso dake kan titin Miller Road a Birnin Kano.

Tsohon gwamnan Kano, Rabi’u Kwankwaso ya wakilci Kano ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin shekarar 2015 zuwa 2019.

Daya daga cikin wadanda suke wajen lokacin da jami’an EFCC suka zo domin rufe ginin, ya gayawa manema labarai cewa jami’an na EFCC sun shaida musu cewa sun rufe ginin ne biyo bayan wani korafi daga wasu daga cikin iyalan tsohon mai bayar da shawara kan tsaro na kasa, Ismaila Gwarzo.

Yace iyalan Ismaila Gwarzo sun yi zargin cewa wani mutum mai suna Abdullahi Muazu Gwarzo, tsohon manajin darakta na tsohuwar hukumar REMASAB a Kano, ya sayar da ginin da yake mallakinsu ne ga Kwankwaso amma yaki biyansu kudinsu. Har yanzu hukumar EFCC bata ce uffan ba dangane da sabon matakin nata.

Leave a Reply

%d bloggers like this: