Dalilan da yasa kotu ta ruguza zaɓen jam’iyyar APC na ɓangaren Ganduje

0 169

Babbar kotin babban birnin tarayya Abuja ta soke zaben da jam’iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje tayi.

A lokacin dayake yanke hukunci mai shari’a Justice Hamza Muazu, ya kuma jaddada zaben da bangaren sanata Ibrahim Shekarau suka gudanar.

Kafin hakan dai akwai rikicin cikin gida tsakanin bangaren tsohon gwamnan na kano da kuma gwamna mai ci na yanzu Abdullahi Ganduje a jam’iyyar ta APC.

Mai shariar ya kuma bukaci bangaren gwamnan akan su dakatar da duk wani mai mukamin zartarwa na jam’iyyar daga bada kowanne umarni koma zartarwa.

Idan za’a iya tinaawa dai bangaren shakekau sun zabi Haruna Ahmadu Danzago a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban jam’iyyar,  yayinda bangarn Ganduje suka zabi Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin shugaba.

Wannan na zuwa adaidai lokacin da kwamitin da jam’iyyar APC ta kafa domin korafe korafe, ya amince da zaben Abdullahi Abbas a matsayin shugaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: