Mutane 10 daga cikin yan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC sun gaza kai banten su, a tantancewar da babban kwamatin ya gudanar a ranakun litinin zuwa jita alhamis cikin makon nans.

Shugaban kwamatin John Oyegun ne ya bayyana hakan a yau juma’a.

A cewarsa yan Takara 13 kawai daga cikin mutane 23 suka tsallake tantancewar da kwamatin ya gudanar.

Haka kuma da aka tambaye shi dangane da jadawalin wadanda suka gaza tsallakewar Mista Oyegun yayi shakulatin bangaro da sunayen, amma yace yan takarar dake da sauran jinni a jika ne kawai suka haye.

Mista Oyegun ya kara da cewa rade-radin da yawo dangane da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan bai samu tantancewar da jam’iyyar ta gudanar ba.

Ana sa ran Wadanda suka tsallake tantancewar zasu kara a zaben fitar da gwani na jam’iyyar da za’a gudanar a tsakanin ranakun 6 zuwa 8 ga watan yunin da muke ciki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: