hakumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gabatar da wasu dokoki gabanin babban zaben 2023 da tafe a badi.

Shugaban hakumar Farfesa Mahmood Yakubu, ya bayyana hakan yau juma’a yayin wani zama tsakanin kwamatin hadin guiwa domin tabbatar da tsaro a babban zaben.

Wanda aka gudanar a hedikwatar hakumar dake birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, hakumar zabe ta kammala tsare-tsaren rumfunar zabukan 2023, watanni 9 kenan gabanin zaben.

Farfesa Yakubu ya kuma bayyana cewa nan bada jimawa ba zasu fitar da jadawalin tsare-tsaren ga yan kasa, yayin da hakumar ta dukufa wajen tabbatar da zaben. Yakubu ya Ambato wasu daga cikin ayyukan da hakumar take yi yanzu haka, da suka hada koyar da yadda za’ayi dangwale, daukar matakan wayar da kai da kuma matakan tabbatar da tsaro da ingancin na’urori da dai sauran su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: