

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, a jiya yace shine cancanci ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Bola Tinubu ya sanar da haka yayin ziyarar da ya kai Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, domin neman hadin kan wakilan jam’iyya, gabannin zaben fidda gwani na jam’iyyar ta APC, inda yace ba dan goyon bayansa ba, shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai zama shugaban kasa ba.
Jigon na APC, wanda yayi jawabi da harshen yarbanci, ya nuni da muhimmiyar rawar da ya taka wajen nasarar jam’iyyar APC 2015.
Bola Tinubu ya bukaci delegates da su kauracewa san zuciya a lokacin da suke gudanar da zaben fidda gwani.
Ya sanar da su cewa ya sadaukar da mukamin mataimakin shugaban kasa da shugaba Buhari ya yi masa tayi a shekarar 2015, inda ya bawa mataimakin shugaban kasa mai ci Yemi Osinbajo.
Daga nan Bola Tinubu ya roki delegates da su zabe shi domin ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na zaben shugaban kasa na 2023.